SHUGABA BUHARI ZAI DAWO GIDA NAJERIYA RANAR LAHADI


Shugaba Muhammadu Buhari zai yi hutun karshen mako a birnin Landan na kasar Ingila, Bayan kammala hutun kwanaki 10 da yaje yi a kasar.

Yayin hutun na sa Shugaba Buhari ya ga likita inda aka sake duba lafiyar kunnensa wanda aka yi masa magani Tun anan gida Najeriya.

A yammacin jiya ne dai Shugaba Buharin ya bayyana wa mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo wannan mataki ta wayar tarho.

Shugaba Buhari na cikin koshin lafiya sa6anin jita-jita da ke ta yawa a kafafen yada labarai na zamani, zai kuma kama aiki a ranar Litinin mai zuwa.

0 Response to "SHUGABA BUHARI ZAI DAWO GIDA NAJERIYA RANAR LAHADI"

Post a Comment