Musa Murtala, Yaro Dan Wattani 20 Da Matar Uba Ta Raunata Ya Sami Kyautar Gida Da Kudi


A safiyar yau din nan ne wata kungiya mai zaman kanta, Mai suna Ibrahim Magnet Foundation, ta ziyarci yaron nan da aka yi wa aika-aika kwanan baya a Kano, ta kuma ba shi kyautar gida na kimamin Naira Milyan Biyar, kana kuma ta ba shi kyautar zunzurutun kudi har Naira Milyan Daya.

A yayin da ya ke gabatar da kyaututtukan, Shugaban Kungiyar Alhaji Ibrahim Sambo, dan asalin Jihar Katsina, mazaunin birnin Tarayya Abuja ya bayyana alhininsa game da abin da ya faru da yaron, sannan ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta daukar mataki don hukunta duk masu hannu kan hakan.

Jaridar LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito cewa, tun da fari, Shugaban Kungiyar ya bukaci Shugabar Kungiyar Arridah Relief Foundation of Nigeria, Hajiya Rabi Salisu, da ta mara wa kungiyar baya, don gabatar da kyaututtukan.

Ita ma mahaifiyar yaron Malama Bilkisu ta bayyana jin dadinta, tare da fatan Allah Ya ba 'danta lafiya, don ci gaba da gudanar da rayuwarsa kamar sauran Yara.

Wakilin Leadership Hausa ya gano cewa Ibrahim Maganet Foundation, kungiya ce da take kan gaba wajen taimakawa marasa galihu a cikin al’umma, tare da kai dauki duk inda ake bukatar hakan.

A halin yanzu dai, al’umma na ci gaba da bayyana takaici da alhininsu kan faruwar lamarin tare da fatar hukumomi za su gaggauta tabbatar da hukunci kan wadanda suka aikata wa yaron haka.

0 Response to " Musa Murtala, Yaro Dan Wattani 20 Da Matar Uba Ta Raunata Ya Sami Kyautar Gida Da Kudi"

Post a Comment