Bismillahi..
Wannan wani Rubutu ne dana taba yi a Jaridar Aminiya ta Ranar 20 ga watan Octoban 2013. Sabo da Muhimmancinsa ne ma naga ya dace na sake Rubutashi. Asha Karatu Lafiya.

Tarihi shi ne rayuwa, fahimtarsa ko gane aukuwarsa ita ce gishirin rayuwar, aiki da abin da tarihin yazo dashi shine abincin rayuwar. Shi ya sa masana ma ke iya ikirarin duk wanda bai san abin da ya faru ba ( a gidansu, ko unguwa ko kauye ko sasa) kafin a haife shi, to tabbas bai san tarihin rayuwarsa ba kuma haka zai kasance tamkar jariri, wato bai san komi game da rayuwa ba. Shi kuwa jariri ai mun san ba kawai rashin sanin abin da ya wakana ba ne ya dame shi, a’a jikinsa da wawalwarsa da yanayin ginuwar rayuwarsa.
Wannan wani Rubutu ne dana taba yi a Jaridar Aminiya ta Ranar 20 ga watan Octoban 2013. Sabo da Muhimmancinsa ne ma naga ya dace na sake Rubutashi. Asha Karatu Lafiya.
Tarihi shi ne rayuwa, fahimtarsa ko gane aukuwarsa ita ce gishirin rayuwar, aiki da abin da tarihin yazo dashi shine abincin rayuwar. Shi ya sa masana ma ke iya ikirarin duk wanda bai san abin da ya faru ba ( a gidansu, ko unguwa ko kauye ko sasa) kafin a haife shi, to tabbas bai san tarihin rayuwarsa ba kuma haka zai kasance tamkar jariri, wato bai san komi game da rayuwa ba. Shi kuwa jariri ai mun san ba kawai rashin sanin abin da ya wakana ba ne ya dame shi, a’a jikinsa da wawalwarsa da yanayin ginuwar rayuwarsa.
Da sanin tarihi zaka iya gane
wane ciki jiya ta samu, kuma me ta Haifa yau kuma da sanin tarihi zamu fahimci
wane irin yara za’a samu gobe. Duk da yake shekaruna baza su wuce ashrin dawani abu ba kuma
bazan iya kiran kaina a matsayin tsarrar Nigeria ba kamar yadda Mahaifina zai
kira. Kasancewa an haifi mahaifina ranar da Nigeria ta samu yancin kai kuma
yana sanar dani abubuwa masu yawa da suka wanzu a zamaninsu. Mafi yawan lokaci
idan yana bani labarin remon democradiya da suyka sha da yadda ake musu gata a
lokacin da suke makaranta sai naji tamkar a wata kasa suka rayu. Na dade ina
mamakin yanayin yadda suka gudanar da makarantarsu cikin jin dadi da kwanciyar
hankali amman mu kuwa ko oho.
Zan iya tunawa a jami’ar mu wani
malami yana bamu labarin rayuwar da sukayi a lokacin suna kanana, daga lokacin
haihuwarsu zuwa lokacin da aka musu kaciya. Ni kuma naka da baki nace da Malam
“Jiya ba yau ba! Lallai Malam kun taso cikin
mani'imciyar rayuwa kai da Nijeriya tsararka. Mu kuwa da muka tsiro a daidai
lokacin da Nijeriyar ta fara kamuwa da masassara (1985-1995), masassarar ta
harbe mu. Domin kuwa abin da zan iya tunawa shi ne a daidai lokacin da aka yi
mana kaciyar, garinmu babu asibitin da likita zai mana shayi, ballantana wani
abu wai shi da wutan lantarki ko ruwan famfo. A gida aka giggille mu da askar
wanzami tamkar yadda aka yi wa kakanninmu. Mun dai dan ci kajin ba laifi;
maganar lantarki da asibiti kuwa ma iya cewa jiya i yau. Bambancin kawai bai
wuce turakun da aka kakkafa mana daure da wayoyi ba, hasken kuma sai mako-mako
kamar sauran yankunan karkara takwarorin namu. Haka batun yake ga ginin
asibiti, amma kiwata lafiyar sai mai Naira. Ruwan famfo kuwa sai in mun yi katarin
shiga birni daidai lokacin da yake kwarara.To, muna fata dai Allah ya warkar da
Nijeriya daga wannan masassara da take fama da ita. Idan kuma ciwon ajali ne,
to Allah ya yi mata kyakkyawar cikawa. Malam kuma Allah ya kara tsawon rai
amin!”
Haka malamin nan yayi murmushi yace:
“Malam Mujahidu kenan. Hakuri za kuyi don wannan kasar sai addu’a don Kullum
abubuwan kara lalacewa yakeyi.”
A shugabancin baya an gina zuciyoyin yan Nigerai ne a matsayin
mutanen da zasu taso su gina kasa, suyi komai ba don amfanin kansu ba sai don
amfanin alummmar kasar nan. Koda yake nima zan iya cewa malaman firamaren mu sun ginamu da wannan
tarbiyar. Don wajajen 1996 zuwa 2000 lokacin ina ajin farko zuwa aji hudu na
makarantar firamare malaman mu sunyi kokari matuka don suga mun tarbiyantu
wajen son al’umma da gina kasa.
A wannan lokaci idan an tambayemu
me muke son mu zama sai kaji kowa na fadan ra’ayinsa. Kamar ni a lokacin ina
cewa ne ina son na zama Likita mai taimakama al’umma. Wani kaji yace yana son
ya zama Dan Sanda mai kare Kasa, Malami mai horror da dalibai ko kuma Dan
Jarida maii taimakon Al’ummma. Haka dai kowa ke fadan ra’ayinsa kuma a lokacin
kowa burinsa kenan amman sai kasha cikin kankanin lokaci tunaninmu ya sauya. A
kwanakin baya na samu wasu yara yan makarantar firamare nake tambayarsu me suke
so su zama nan gaba. Sai daya yayi sauri yace shi yana son ya zama shuganan
kasa ne, wani kuma yace gwamna.
Ya salam! To ya akayi cikin kankanin lokaci tunanin kowa ya
sauwa. Abin ba’a yara kawai ya tsaya ba. Mu kanmu yanzu mafiyawan ‘yan ajinmu
munje muna karatu a inda mukasan zamu samu kudi da yawa. Mafi yawa daga cikin
mu basa tunanin kudin ta wace hanya zai fit aba. Hallas ko haram.
Abuwa masu dadi
sun faru lokacin da Nigeria take da
shugabanni maso kishinta. Wutan Nepa, kiwon lafiya, makarantu, walwalan jama’a
da sauransu. Amman mu a zamaninmu mun samu akasin haka. Idan kace zakayi
makaranta to akwai yajin aiki, idan kasuwanci ne to kasa ba tsaro. Haka batun
yake ga wadanda suka gama karatun don babu aikin yi. To yanzu me ake son dan
kasar nan yayi. Idan kayi Magana ace baka da kunya, idan kayi shiru ace bakasan
yancin kanka ba. Idan kayi zabe baka ganin abin daka zaba sai abin da manyan mu
suka zabar mana.
Matsalolin haka
suke faruwa karuwa kullum. Amman a kowane haquri akwai nasara amman duk alummar
data manta Allah dole Allah ya manta da ita. Kowa zai iya gina rayuwarsa a inda
yake ganin ya dace dashi amman mafi kyawun rayuwa shine rayuwa da tsoron Allah.
Muyi ma kanmu guzuri don mafi kyawun guzuri shine Imani. Allah ya tsare kasarmu
da mutanan cikinta.
Alhamdulillahi...
razer surround pro
ReplyDelete