Bismillahi
Qur'ani da Ilimin kimiyya sun hadu a wajaje da yawa. Qur'ani littafi ne da aka saukar dashi tun kafin zuwan Ilimin Kimiyya da wajen shekara dubu amman abin farin cikin sai gashi ilimin masu kimiyya yana zuwa daidai dana Qur'ani. Asha Karatu Lafiya.

Qur'ani da Ilimin kimiyya sun hadu a wajaje da yawa. Qur'ani littafi ne da aka saukar dashi tun kafin zuwan Ilimin Kimiyya da wajen shekara dubu amman abin farin cikin sai gashi ilimin masu kimiyya yana zuwa daidai dana Qur'ani. Asha Karatu Lafiya.
Tsarin
Kur’ani Wajen Tabbatar da Ilimi
Ga duk wanda ya saba
karanta Kur’ani mai girma, ya kuma fahimci sakon da yake kokarin isarwa ga mai
karatunsa, zai ga cewa littafi ne mai neman shiryar da mai karatu ta hanyoyi
masu sauki, wadanda mai karatun zai iya bi don ya shiryu. Littafi ne mai dauke da dimbin ilimi wanda
Allah kadai ya san yawansu. Littafi ne
mai dauke da usulubi mai dadi wajen karatu da karantarwa. Manyan hanyoyin da Kur’ani ke amfani dasu
wajen tabbatar da dalilan Kimiyya sun kunshi hanyar gani, ko kallo, da nazari
ko tunani, da kuma tabawa. Sauran
hanyoyin sun hada da hakawa, ko tonawa (don ganin yadda abu yake), da haurawa,
da gangarawa, musamman kan abinda ya shafi sararin samaniya da sauran duniyoyin
da ke makwabtaka da tamu. Ga duk wanda
ya bi wadannan hanyoyi, zai iya fahimtar sirrin da ke cikin halittan sama da
kasa da taurari da wata da rana da karkashin kasa da hazo da ruwan sama da iska
da sanyi da zafi da tsarin halittan dabbobi da na dan Adam, da dai sauran
abubuwan da Allah Ya watsa a wannan duniya tamu.
Duk wani abinda malamin
kimiyya zai karanta ko yi nazari a kai, Kur’ani ya tabo bayani a kanshi, ya
kuma kalubalance shi da ya duba ya gani, ko yayi tunani a kai, ko kuma ya hango
ya gani, da dai sauran hanyoyin kalubale.
In ya ga dama kada ya fara yin imani sai ya tabbatar da gaskiyar abinda
aka sanar dashi. Amma kuma da zarar ya
fahimci gaskiya, to fa hujja ta tabbata a gareshi ko a kanshi. Wannan ya sha banban da tuhumar da sauran
masu akidu ke yi wa Musulmai, cewa: muslims
are too dogmatic. Ma’ana, musulmi
mutane ne masu yawan yarda da abu kawai ba tare da sun san hakikaninsa ba. Wannan kalma suna fadinta ne a babin zargi ba
yabo ba, ga dukkan musulmi. Suna ganin
musulunci bai baiwa mutane damar kalubalantar abinda ya fada a Kur’ani ba. Masu wannan kalami sun jahilci addinin gaba
daya. Da sun karanta Kur’ani sosai, da
basu fadi haka ba. Ga misali nan guda
daya, inda Allah ke cewa:
“Lalla ne, a cikin
halittan sammai da kasa, da sabawar dare da yini da jirage wadanda suke gudana
a cikin teku (dauke) da amfanin mutane, da abinda Allah Ya saukar daga sama na
ruwa, sai ya rayar da kasa da shi bayan mutuwarta, kuma ya watsa cikinta daga
dukkan dabbobi, da kuma juyawar iskoki da girgije horarre a tsakanin sama da
kasa; hakika akwai ayoyi ga mutane masu hankalta.” (Bakara: 164)
Wannan aya, kamar yadda
malaman tafsirin Kur’ani suka tabbatar, ta kumshi dukkan nau’ukan ilimin
kimiyya da dan Adam ke alfahari dashi a yau.
Daga ilimin Fiziya (Physics), zuwa ilimin sinadaran da ke tsakanin sama
da kasa (Chemistry), zuwa ilimin kasa (Geography), da ilimin halittu (Biology),
da na tsirrai (Botany), da na teku (Oceaonology), da ilimin tsarin sadarwa
(Communication), da na sararin samaniya (Astronomy), da tattalin arzikin kasa,
da sauran nau’ukan ilimin da sai mai bincike ya bincika zai gano su. Abin sha’awa shine, da Allah Ya gama sanar da
mai karatun wannan aya tsarin halittan da yayi a ciki, sai yace “…hakika akwai
ayoyi ga mutane masu hankalta.” Wannan
kuwa ke nuna cewa in har ka hankalta, to za ka ga abinda Allah ke ikirarin ya
sanya ko halitta. A takaice dai wannan
na nufin duk abinda Allah ya fada abubuwa ne da ake iya ganinsu da ido, ko iya
hankaltar tsarinsu da irin abinda ke cikinsu na mamaki da al’ajabi.
Duk da dimbin ilmin da
ke cikin wannan littafi mai girma, mai karatu zai yi mamakin jin cewa
Al-Kur’ani ba littafin kimiyya bane, balle na ilimin kasa. Ba littafin koyar da sadarwa bane kadai..a a,
littafin shiriya ne. Duk abinda ka gani
a ciki wanda ya shafi wani ilimi, riban kafa ne kawai. Amma asali Allah Ya kawo
shi ne don dan Adam ya fita daga kangin bauta wa wani halitta makamancinsa,
zuwa ga bauta wa wanda ya halicce shi kadai, shine Allah. Wannan tasa tsarin littafin yake a sura-sura,
ba wai babi-babi mai Magana a kan wani nau’in ilimi ba. Sabanin sauran littafan kimiyya, inda
marubucinsu ke shirya littafin zuwa babi-babi kan abinda yake son
karantarwa. Don haka Kur’ani littafin
addini ne da shiriya. Duk abinda ka samu
a cikin wanda ke karantar da kai wani ilimi na neman abin duniya ko amfanin
rayuwa, to riba ne da Allah ya sanya a ciki.
Idan ka kara imani da abinda ke ciki, sai ka fi amfana da ribar fiye da
kowa. Wannan tasa sauran masu binciken
Kimiyya masu lekawa cikin Kur’ani suna dauko abinda ya dace da iliminsu suna
sauya masa tsari don neman suna a duniya, ribarsu kadan ne in ka kwatanta da na
wanda yayi imani da littafin. Wannan, a
takaice, shine tsarin da Kur’ani ke bi wajen kiran mai bincike yayi bincike
cikin abinda aka fada cikin littafin, don gano gaskiyar abinda aka sanar dashi
a ciki.
A nasu bangaren, malaman kimiyyar zamani na
bin hanyar bincike ne na kwakwaf, don tabbatar da abinda ake ikirari a
kai. Hanyoyin bincikensu na nan da yawa,
kamar yadda muka sani. Suna amfani da
na’ura a dakin bincike, da na’urar hangen nesa, da wanda suke kafawa a wajen da
suke binciken. Har wa yau suna amfani da
tsarin dauko abinda suke son bincike don yin nazari a kansa, kai tsaye. Bayan haka, suna da ka’idoji da suke amfani
da su (watau Scientific Methodology) wajen
tantance abinda suka samu
na sakamako a yayin da suke binciken.
Sannan su basu yarda da duk abinda ba a ji ko gani ko iya taba shi
ba. Duk abinda ake iya hankalta ko ji ko taba shi kadai suke
la’akari da shi. Sannan a galibin lokuta
sukan samu sakamako na wucin-gadi, wanda suke amfani dashi don ci gaba da wani
binciken. Bayan haka, saboda
kasancewarsu ‘yan Adam ne masu tawaya, ba dukkan lokuta ko bincike suke gano
abinda yake daidai ko gaskiyar abinda suke nema ba. Wannan tasa kafin su binciken sai sun tsara
wasu nau’ukan hasashe (watau Hypothesis) da
zasu musu jagora wajen samun irin sakamakon da suke bukata. Wannan, a takaice, shine tsarin da malaman
kimiyya ke bi wajen gudanar da bincikensu a kimiyance. Addini da al’ada basu tasiri wajen bincikensu
ko kadan. “Zahiri”, shine abinda suka
sani. Allah mana jagora!
Alhamdulillahi... Zamuci GAba
0 Response to "KIMIYYAR KUR’ANI DA TA ZAMANI: A INA AKA HADU (Na Daya)"
Post a Comment