Gwamnatin Tarayya, karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta kaddamar da kwamiti na musamman don bunkasa harkar noman shinkafa da kuma alkama a kasar nan.
A ranar Larabar da ta gabata ne Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da kwamitin a ofishinsa dake fadar Shugaba Kasa a Abuja.
Kamar yadda Farfesa Osinbajo ya bayyana a yayin da yake kaddamar da kwamitin ya ce, abinda ake fatan wannan yunkurin ya cimma shi ne ganin noma ya zama a sahun farko a bisa kokarin da gwamnati ke yi don ganin an farfado da tattalin arzikin kasar nan.
“Gwamnatin Buhari ta bawa noma matukar muhimmanci, musamman noman shinkafa da alkama, babbar manufar mu ita ce, ya kasance cikin shekara daya mu nunawa duniya lallai da gaske muke yi.” In ji Osinbajo.
Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ne aka dora wa alhakin jan ragamar kwamitin, yayin da Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Ebonyi, Injiniya Dabid Umahi, Ministan Harkokin Noma, Cif Audu Ogbeh da sauran su za su kasance a matsayin membobin kwamitin.
0 Response to "An Kaddamar Da Kwamitin Bunkasa Noman Shinkafa Da Alkama"
Post a Comment