Takaitaccen Jawabin Da Shugaba Muhammadu Buhari Ya Gabatar Kan Cika Shekara Daya Akan Mulki

May 29,2016.

1. Shekara daya kenan da zuwan mu, cikin wannan lokaci an samu nasarori, jarjejenjiya, kunci da kuma aiki tukuru. Sai dai nayi imanin zamu dauki darasi daga abubuwan da suka faru don taimaka mana wajen tabbatar da ci gaban Nijeriyar da muke fata.

2. Daga zuwan mu, farashin danyen man fetur ya karye a kasuwar duniya, a baya ana saida kanga daya sama da dalar Amurka 100 amma da muka zo ya fadi zuwa kasa da da dala 30, kuma gwamnatocin baya ba su yi tanadi don irin wannan lokaci ba.

3. Mun zo mun samu kasa cike da basussuka da 'yan kwangila ke bi, haka jihohi 27 ciki 36 ba sa iya biyan albashi, ga kuma rashin tsaro a Arewa maso Gabas inda kananan hukumomi 14 ke karkashin 'yan Boko Haram, muna zuwa mun kalli wadannan abubuwa, kuma zuwa yanzu mun samu nasarar karbe duk wani sashen naNijeriya daga hannun 'yan ta'adda, mun taimakawa jihohi da kudaden da suke biyan ma'aikatan su, sannan mun biya mafi yawan basussukan da 'yan kwangila ke bi.

4. Domin ceto tattalin arzikin mu, gwamnati za ta fi maida hankali kan noma, masana'antum cikin gida gwamnati za ta taimaka musu su fara aiki, duk a shirye gwamnati take ta bawa manoma duk gudunmawar da ta kamata.

5. A bangaren yaki da cin hanci da rashawa kuwa, mun ba hukumar EFCC cikakken 'yancin na tuhumar barayin gwamnati sannan mun ankarar da bangaren shari'a gameda muhimmancin yin adalci da hukunta duk wadanda aka samu da laifuka.

6. Mun dauki matakin karin kudin fetur ne da kuma tsaurara dokokin musayar kudadedon ganin mun ceto kasar nan daga ci gaba da fuskantar tabarbarewar tattalin arziki tare kuma da gaggauta gyara matatun man fetur ta yadda za mu dogara da kan su.

7. Mun bullo da tsarin asusun bai-daya wato TSA ne don dakile hanyoyin da manyan jami'ai da hukumomin gwamnati ke satar kudin jama'a kuma akan wannan tsari ne muka iya gano ma'aikatan bogi har dubu 43,000, wanda hakan yake bawa gwamnati damar ajiye naira bilya 4.5 a duk wata.

8. Game da kasafin kudi, tsawon rayuwa ta ban taba sani wata almundahana da yin aringizo a kasafin kudi ba sai a wannan karo wanda a kan haka ne ya sa muka fitar dawani tsarin kasafin kudi da ba a taba yin irin sa inda muka bayar da fifiko kan ayyukan raya kasa da sama da kaso 30%.

9. Manoma na kokawa game da karancin takin zamani da saura kayayyakin aikin noma wanda a kan haka gwamnati ta yi kwakkwaran tanadi da zai taimaka ta yadda za a samu amfani mai albarkatun musamman ma a bangaren noman shinkafa. Ina jinjinawa mata da su ma suke bada tasu gudunmawar a wannan bangare.

10. Cikin kasafin kudin bana akwai gurbin da za mu samar da guraban aiki ga miliyoyin 'yan Nijeriya ciki har da malaman makaranta dubu 500,000.

11. Game da Neja Delta, za mu amfani da rahoton matsalisar Dinkin Duniya wajen share turbayar yankin wanda hakan zai taimaka wajen ciyar da yankin gaba. Mun kuma ba wa rundunar soja umarnin kaddamar da yaki kan tsagerun Neja Delta wandake fasa bututun mai a halin yanzu, duk wadannan ke da hannun a ciki za su fuskanci fushin hukuma.

12. Ina jinjinawa al'ummar Nijeriya bisa irin juriya da hakuri da suka nuna na irin halinkuncin da gwamntocin da suka gabata suka Jefa su.

13. Zan so na rufewa da abun farin ciki, na kubutar da 'yan Nijeriya da sojojin mu suke yi a kullum ciki har da biyu daga 'yan matan Chibok, a kullum ina tunawa da su, kuma ba zamu gajiya ba har sai mun kubutar da dukkan wadanda suke hannun 'yan ta'addan.

14. Ina gode muku, ina kuma rokon ku ci gaba da ba wa wannan gwamnati goyon baya, wajen gyara da ciyar da Nijeriya gaba.

- Muhammadu Buhari
Shugaban Kasar Nijeriya.

0 Response to "Takaitaccen Jawabin Da Shugaba Muhammadu Buhari Ya Gabatar Kan Cika Shekara Daya Akan Mulki"

Post a Comment